Kungiyar Hamas Ta Soki Taron Kasashen Larabawa A Kasar Saudiyya
Mahmud al-Zahhar wanda kusa ne a kungiyar gwagwarmayar Hamas ya ce; Sakamakon taron ba amsa bukatun al'ummar palasdinu ba
Mahmud al-Zahhar ya kara da cewa; Rashin bijiro da batun hakkin palasdinawa na komawa zuwa kasarsu da korar 'yan mamaya daga Kudus, yana nuni da mummunar rawar da Saudiyya take takawa.
Al-Zahhar ya nuna takaicinsa akan yadda Saudiyya take bunkasa alakarta da haramtacciyar Kasar Isra'ila sannan ya kara da cewa: Saudiyyar tana daukar wannan matakin ne bisa amincewar sarki Salman Bin Abdulaziz, kuma a lokacin da Amurka ta fito da shirin da ake kira; Yarjejeniyar Karni.
Yarjejeniyar karni dai ta shafi kawo karshen hakkokin palasdinawa da bai wa haramtacciyar kasar Isra'ila cikakkiyar damar iko akan dukkanin palasdinu.