Nijar : An Rufe Wuraren Kwanan Dalibai Na Jami'ar Yamai
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30086-nijar_an_rufe_wuraren_kwanan_dalibai_na_jami'ar_yamai
Ma'aikatar ilimi mai zurfi a Nijar, ta sanar da rufe wuraren kwanan dalibai na jami'ar Abdul Mummuni Diafo dake Yamai babban birnin kasar, bayan artabun da ya faru yau Laraba tsakanin dalibai da jami'an tsaro.
(last modified 2018-08-22T11:31:43+00:00 )
Apr 18, 2018 18:22 UTC
  • Nijar : An Rufe Wuraren Kwanan Dalibai Na Jami'ar Yamai

Ma'aikatar ilimi mai zurfi a Nijar, ta sanar da rufe wuraren kwanan dalibai na jami'ar Abdul Mummuni Diafo dake Yamai babban birnin kasar, bayan artabun da ya faru yau Laraba tsakanin dalibai da jami'an tsaro.

Sanarwar ta ce an rufe wuraren kwanan har sai al'amura sun daidaita, amma wuraren daukar karatu da motocin jigilar dalibai zasu ci gaba da aiki, don kada a tsaida karatun na bana.

kawo yanzu an bayyana samun dalibai masu yawa da suka jikkata da kuma samun barna mai yawa a cikin jami'ar, za'a kuma gudanar da bincike don gano duk masu hannu a wannan rikici don gurfanar dasu gaban shari'a.

Al'amuran karatu dai sun shiga cikin wani mawuyacin yanayi a jami'ar ta Yamai, inda daliban suka gudanar da zanga-zanga yau don nuna adawa kan mummunan halin rayuwa da kuma karatunsu ke ciki, wanda suka ce har yanzu hukumomin kasar sun kasa magance shi.