Shugaban Burundi Ya Gudanar Da garambawul A Cikin Majalisar Ministocin Kasar
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya gudanar da wani garambawul a cikin majlaisar ministocin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a cikin wata sanarwa da ofishin shugaban kasar Burundi ya fitar, an sanar da cewa shugaban kasar ta Burundi Pierre Nkurunziza, ya sauya ministoci hudu daga cikin ministocin kasar, kuma maye gurbinsu da wasu na daban, inda kuma ya kara ministan guda, a cikin majalisar, wadda ta shi daga ministoci 20 zuwa ministoci 21.
Daya daga cikin abin da ya fi jan hankalia sauye-sauyen da shugaban kasar ta Burundi ya yi dai shi ne, yadda lamarin ya shafi har da ministan harkokin wajen kasar.
Tun daga watan Afrilun 2015 ce dai aka fara samun matsaloli na siyasa akasar Burundi, bayan da shugaban kasar ya kudiri aniyar zarcewa kan karagar mulki a wa'adi na uku, wanda ya saba wa dokar tsarin mulkin kasar.