Madugun 'Yan Adawan Kongo Ya Musanta Cimma Yarjejeniya Da Shugaba Kabila
(last modified Wed, 25 Apr 2018 05:26:29 GMT )
Apr 25, 2018 05:26 UTC
  • Madugun 'Yan Adawan Kongo Ya Musanta Cimma Yarjejeniya Da Shugaba Kabila

Madugun 'yan adawan kasar Demokradiyyar Kongo, Felix Tshisekedi, yayi watsi da wasu labarai da ke cewa yana shirin cimma yarjejeniya da shugaban kasar ta Kongo Joseph Kabila wanda ke fuskantar matsin lambar ya sauka daga karagar mulki.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar madugun 'yan adawan ya bayyana hakan ne a wani jawabin yakin neman zabe da yake yi a kasar inda yayi watsi da abin da ake yadawa na cewa zai karbi matsayin firayi minista, kamar yadda a baya shugaba Kabilan ya gabatar wa 'yan adawan don dai su amince da kokarinsa na ta zarce.

Mr. Tshisekedi ya ce jam'iyyarsu ta zabe shi ne a matsayin dan takarar shugaban kasar, don haka bai ga dalilin da zai amince da matsayin firayi minista ba, yana mai cewa zai ci gaba da tsayawa a matsayin dan takararsa har ya sami nasara a zaben da za a gudanar din.

Mr. Tshisekedi yana daga cikin 'yan takara biyu, wato tare da fitaccen attajirin nan Moise Katumbi da za su tsaya a zaben shugaban kasar da aka jinkirta wanda za a gudanar da shi a watan Disamba mai zuwa. To sai dai kuma ana ganin da wuya ya kai labari ganin cewa da dama daga cikin 'yan adawan sun shiga cikin gwamnatin bayan mutuwar tsohon madugun 'yan adawan kasar Etienne Tshisekedi, mahaifin Felix din a shekarar bara.