Kasar Habasha Za Ta Kayyade Wa'adin Mulkin Firayi Minista A Kasar
Sabon firayi ministan kasar Habasha (Ethiopia), Abiy Ahmed, ya sanar da aniyarsa ta yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar da nufin kayyade wa'adin mulkin firayi minista a kasar zuwa wa'adi biyu kacal.
Kafar watsa labaran Africanews ya bayyana cewar firayi minista Abiy Ahmed ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a garin Hawassa, babban birnin lardin Kudancin kasar inda ya ce ya fara kokari wajen ganin an takaita wa'adin mulkin firayi minista a kasar zuwa wa'adi guda biyu kacal.
A bisa tsarin mulkin na yanzu dai babu wani wa'adi na mulki da aka kayyade wa matsayin firayi minista a kasar Habashan da ke amfani da tsarin mulki na majalisa inda jam'iyyar da take da rinjaye a majalisar take da hakkin ayyana mutumin da zai zama firayi ministan kasar.
Firayi ministan Abiy Ahmed dai yana ci gaba da rangadin da ya faro ne zuwa larduna da yankuna daban-daban na kasar tun bayan da ya dare karagar mulki a ranar 2 ga watan Aprilun nan bayan murabus din da tsohon firayi ministan Hailemariam Desalegn.