An Kai Hari Kan Jami'an Tsaron Nijer A Jahar Difa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30452-an_kai_hari_kan_jami'an_tsaron_nijer_a_jahar_difa
Wata majiyar yankin Difa ta sanar da cewa wasu mahara da ake zaton 'yan boko haram ne sun kai hari kan wani sansanin jami'an tsaro a kusa da kan iyakar kasar da Najeriya
(last modified 2018-08-22T11:31:46+00:00 )
Apr 30, 2018 19:16 UTC
  • An Kai Hari Kan Jami'an Tsaron Nijer A Jahar Difa

Wata majiyar yankin Difa ta sanar da cewa wasu mahara da ake zaton 'yan boko haram ne sun kai hari kan wani sansanin jami'an tsaro a kusa da kan iyakar kasar da Najeriya

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar Sin ya nakalto wata majiyar yankin Difa na cewa a daren jiya lahadi wasu mahara da ake kyautata zaton 'yan boko haram ne sun kai hari kan wani sansani na jami'an tsaron kasar dake kusa da kan iyakar kasar da Najeriya, inda suka yi awan gaba da wasu motocin soja da dama.

Saidai, majiyar ba ta yi karin haske ba, kan yawan motocin da maharan suka yi awan gaba da su.

Duk da irin ci gaban da aka samu wajen dawo da kwanciyar hankali a jahar, to amma har yanzu ana ci gaba da fuskantar hare-hare nan da can da kauyukan dake cikin jahar.

Kimanin shekaru uku kenan da yankin Difa na kudu maso gabshin Nijer mai iyaka da arewa maso gabshin Najeriya ke fuskantar hare-haren kungiyar ta'addanci Boko Haram.

Tun a shekarar 2009 ne kungiyar Boko haram ta fara kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya, kafin daga bisani ta fadada kai hare-haren a kasashen Kamaru, Tchadi da jamhoriyar Nijer, lamarin da ya sanya kasashen suka kafa rundunar hadin gwiwa domin tunkarar mayakan na Boko haram.