Moroko Ta Sanar Da Yanke Huldar Diplomasiyya Da Iran
Gwamnatin ta Moroko ta tuhumi Iran da cewa tana taimakawa kungiyar yammacin Sahara ta Polisariyo, don haka ta sanar da yanke huldar diplomasiyya da Iran
Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Moroko ta fitar a yau talata ta kunshi rufe ofishin jakadancin kasar a nan Tehran, tare kuma da kiran jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran da ya bar kasar ra Moroko.
Gwamnatin kasar ta Moroko ta riya cewa kungiyar HIzbullah ta Lebanon tana ba da horo ga mayakan Polisariyo a yankin yammacin sahara.
Kungiyar Polisariyo na kai ruwa rana da gwamnatin Moroko ne akan hakkin iko da yammacin sahara wanda Morokon ta shiga ciki tun 1975.
A watannin baya kungiyar ta sanar da cewa a shirye take ta yi tattaunawa ta kai tsaye da gwamnatin Moroko.