Piraminstan Kasar Gabon Ya Yi Murabus
(last modified Wed, 02 May 2018 10:56:11 GMT )
May 02, 2018 10:56 UTC
  • Piraminstan Kasar Gabon Ya Yi Murabus

Bayan matakin da kotun tsarin milkin kasar Gabon ta dauka na kawo karshen Majalisar dokokin kasar, gwamnati ta gabatarwa Shugaban kasar murabus dinta

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a jiya Talata, Piraministn kasar Gabon Emmanuel Issoze Ngondet ya gabatar da murabus din gwamnatinsa ga shugaban kasar Ali Bongo Ondimba.

Wannan bukata ta murabus din gwamnatin kasar Gabon na zuwa ne kwana guda bayan da kotun tsarin milkin kasar ta dauka na rusa majalisar dokokin kasar.

A ranar Litinin din ta gabata ce kotun kare tsarin milkin kasar Gabon ta rusa majalisar dokokin kasar tare da bukatar gwamnati ta yi murabus biyo bayan kasawarta na gudanar da zaben 'yan Majalisar shekaru biyu da kawo karshen wa'adinta.

Bisa dokar kundin tsarin milkin kasar Gabon, Majalisar dattijan kasar ce za ta gudanar da ayyukan 'yan majalisar dokoki kafin a gudanar da zaben 'yan majalisar.