Nijar : Masarautar Maradi Ta Hana Bidi'o'i A yayin Bikin Aure
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30508-nijar_masarautar_maradi_ta_hana_bidi'o'i_a_yayin_bikin_aure
Masarautar Katsinan Maradi ta jamhuriyar Nijar ta bi sahun takwarorinta na Azbin da Damagaram wajen hana Bidi'o'i a yayin bikin aure.
(last modified 2018-08-22T11:31:47+00:00 )
May 03, 2018 05:35 UTC
  • Nijar : Masarautar Maradi Ta Hana Bidi'o'i A yayin Bikin Aure

Masarautar Katsinan Maradi ta jamhuriyar Nijar ta bi sahun takwarorinta na Azbin da Damagaram wajen hana Bidi'o'i a yayin bikin aure.

Dokokin sun hada da soke kayan gara, da yawan shakatawa da kide-kide na Orchestre « koumshi » da Damu » da dai saurensu, saidai masarautar ta ce kudin sadaki da yake a jikka 33, kwatamcin dalar Amurka 60 ya danganta da halin da mutum yake dashi idan zai kara wannan ya shefe shi, idan bai da hali kuma babu cilastawa.

An dauki wannan kudurin ne bayan wani bincike da wata kungiya mai suna ''Madallah'' ta gudanar na yadda bukukuwa ke son gagarar mai karamin hali a 'yan shekarun baya bayan nan.

Binciken ya gano cewa irin wadannan bidi’o'in, sukan tilasta wasu zuwa su ciyo bashi domin suyi abinda bai zama dole ba a addini.