Wasu 'Yan Ta'adda Sun Kashe Abzinawa 16 A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30514-wasu_'yan_ta'adda_sun_kashe_abzinawa_16_a_mali
Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun hallaka Abzinawa 16 a arewacin kasar Mali, kwanaki kadan bayan kashe mutane 40 da akayi a wasu kauyukan kasar dake kusa da kan iyaka da kasar Nijer.
(last modified 2018-08-22T11:31:47+00:00 )
May 03, 2018 11:49 UTC
  • Wasu 'Yan Ta'adda Sun Kashe Abzinawa 16 A Mali

Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun hallaka Abzinawa 16 a arewacin kasar Mali, kwanaki kadan bayan kashe mutane 40 da akayi a wasu kauyukan kasar dake kusa da kan iyaka da kasar Nijer.

Magajin Garin Menaka,ya ce an kai harin ne daren Talata da ta gabata a kauyen Tindibawen dake da nisan kilomita 160 daga garin Menaka dake kusa da iyakar Nijar,tare da tabbatar da mutuwar mutane 16.

Kafin kai  harin, mayakan sa kai na Azbinawa sun bayyana cewa, mayakan ‘yan ta’addan sun yiwa wasu fararen hula 17 kisan gilla a matsayin hukunci, ciki harda tsofaffi, tare da kone gidajensu.

A kwanakin baya-haren ana samun karuwar hare-haren ta'addanci a kasar ta Mali, kasancewar mayaka dake da’awar jihadi da a baya suka fi karfi a arewacin kasar, a yanzu sun bazu zuwa yammacin kasar, inda suke yin amfani da rikicin kabilanci tsakanin Fulani makiyaya da Azbinawa makiyaya wajen kai hare-haren.