Jami'an Tsaron Masar Sun Hallaka 'Yan Ta'adda 15 A Yankin Sina
Majiyoyin tsaron kasar Masar sun ba da labarin cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasarar hallaka wasu 'yan ta'adda su 15 a wani hari ta sama da sojojin kasar suka kai musu a wata tungarsu da ke yankin Sina.
A rahoton da tashar talabijin din Sky News Arabic ta bayar ta jiyo wasu majiyoyin tsaron kasar Masar din suna cewa sojojin sun kai harin ne a wasu yankuna guda biyu da suke yankin Al-Arish da kuma helkwatar yankin na Sina' inda suka hallaka 'yan ta'adda kimanin 15.
Tun a watan Fabrairun da ya gabata ne dai sojojin kasar Masar din bisa goyon bayan 'yan sandan kasar suka kaddamar da wasu jerin hare-hare da suka ba shi sunan "Sina 2018" da nufin fatattakan 'yan ta'addan daga yankin inda suka sami nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama da kuma kama wasu.
Yankin na Sina' dai ya zama wata tunga ta 'yan ta'adda a kasar ta Masar duk kuwa da kokarin da gwamnatin kasar take yi na korarsu daga wajen.