Burundi: Mutane 26 Sun Hallaka A Arewa Maso Yammacin Kasar
(last modified Sat, 12 May 2018 19:29:44 GMT )
May 12, 2018 19:29 UTC
  • Burundi: Mutane 26 Sun Hallaka A Arewa Maso Yammacin Kasar

A Wani hari da wani gungu masu dauke da makamai suka kai wasu kauyuka na arewa masu yammacin kasar Burindi, kimanin mutane 26 suka rasa rayukansu yayin da wasu 10 na daban suka jikkata

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Ministan kula da harkokin tsaro na al'ummar kasar Alain Guillaume na cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari kauyen Cibitoke kusa da iyakar kasar da jamhoriyar Demokaradiyar Kwango, tare da kashe mutane 26 da kuma jikkata wasu 10 na daban.

Har ila yau Ministan ya ce maharan sun kone gidajen kauyen kurmus.saidai ya zuwa yanzu mahukuntan kasar ta Burundi ba su bayyana dalilin da ya sanya aka kai wannan hari ba.

Tun a shekarar 2015 ne kasar Burundi ta fada cikin rikicin siyasa bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya bayyana aniyarsa na zarcewa a kan karagar milki.

A halin da ake cikin kasar na fuskantar matsalar tattalin arziki da zamantakewa saboda rashin kudaden waje da kuma Man fetir.