Rikici Ya Hallaka Mutane 15 A Burundi
Kungiyar kare hakin bil-adama ta sanar da hallakar mutane 15 yayin wani rikici da ya kuno kai a lokacin yakin zaben raba gardama kan tazartan shugaba Nkurunziza.
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto kungiyar kare hakin bil-adama ta kasar Burundi cikin wani bayyani da ta fitar a wannan juma'a ta ce bayan mutane 15 din aka kashe akwai wasu karin takwas da aka yi awan gaba da su.
Sanarwar ta ce 'yanbangar gwamnati da jami'an tsaron kasar ke mara wa baya na ci gaba da firgita 'yan adawa da kuma sanya tsoro a zukatan al'ummar kasar kafin gudanar da zaben raba gardama na yi wa kundin tsarin milkin kasar kwaskwarima.
Shidai wannan zabe zai baiwa shugaba Pierre Nkurunziza damar ci gaba da zama kan karagar milki har zuwa shekara ta 2034.
Idan ba a manta ba dai a watan Avrilun 2015 ne shugaba Pierre Nkurunziza ya bayyana shirinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a karo na uku, lamarin da ya janyo ce-ce ku-ce da rikcin siyasa har ta kai ga hasarar rayuka da dama da kuma gudun hijra na wasu dubun 'yan kasar zuwa ketare.