Kasashen Sudan Da Masar Zasu Karfafa Dangantaka A Tsakaninsu.
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31252-kasashen_sudan_da_masar_zasu_karfafa_dangantaka_a_tsakaninsu.
Shugaban kasar Masar Abdulfatah Sisi da ministan harkokin wajen kasar Sudan sun gana a tsakaninsu, inda bangarorin biyu suka amince da karfafa dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu.
(last modified 2018-08-22T07:01:54+00:00 )
May 30, 2018 02:29 UTC
  • Kasashen Sudan Da Masar Zasu Karfafa Dangantaka A Tsakaninsu.

Shugaban kasar Masar Abdulfatah Sisi da ministan harkokin wajen kasar Sudan sun gana a tsakaninsu, inda bangarorin biyu suka amince da karfafa dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu.

Majiyar Muryar Jumhuriyar Musulunci ta Iran daga birnin Alkahiran Masar tana cewa a ganawar Abdulfatah Sisi da Mohammad Ahmad ministan harkokin wajen kasar Sudan, sun tattauna batun lamuran da suka shafi kasashen biyu a yankin gabas ta tsakiya. 

A karshen ganawar dai Ministan harkokin wajen kasar Sudan ya bayyana cewa shugaban kasar Masar Abdulfatah Sisi zai ziyarci kasar Sudan a cikin watan Octoba na wannan shekara  inda bangarorin biyu zasu rattaba hannu kan wasu yerjeniyoyi na karfafa dangantakar kasashen biyu. 

Kasashen Sudan da Masar dai suna da sabanin kan niyakar kasashen biyu, sunnan sun damu da gina madatsar ruwa ta Annahda wacce gwamnatin kasar Ethiopia take ginawa kan kogin Nilu, wanda ake ganin idan an kammala za ta jawo karancin ruwa a kasashen Sudan da Masar.