Kotu ta yi wa Hama Amadou sakin talala a Nijar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3139-kotu_ta_yi_wa_hama_amadou_sakin_talala_a_nijar
Da safiyar jiya Talatar ce kotun daukaka kara a birnin Yamai ta amince da yi wa Hama Amadou sakin talala.
(last modified 2018-08-22T06:58:03+00:00 )
Mar 30, 2016 00:09 UTC
  • Kotu ta yi wa Hama Amadou sakin talala a Nijar

Da safiyar jiya Talatar ce kotun daukaka kara a birnin Yamai ta amince da yi wa Hama Amadou sakin talala.

Kamfanin dillancin Labaran kasar Faransa ya nakalto Lauyan da ke kare Hama Amadou Boubakar Mossi na cewa wannan mataki da kotun ta dauka babu wata tantama cikinsa daga yanzu Hama Amadu yana da izinin zuwa inda ya ga dama. Hama Amadou da ya kasance a matsayin dan takara a zaben shugaban kasar ta Nijar tun a zagaye na farko har kuma ya samu zuwa zagaye na biyu, ya sha neman a yi masa sakin talalan amma abin ya ci tura, inda ma daga bisani wani rishin lafiyar da ya fara yayin da yake tsare a gidan Kaso ya yi sanadiyyar ficewarsa zuwa kasar Faransa domin yi masa magani a wata asibicin Amurka dake birnin Paris.

Malan Hama Amadu dai shi ne dan takara na farko a jumhoriyar Nijer wanda ya zo zagaye na biyu yana tsare a gidan Kaso.