An Hallaka 'Yan Tawaye 9 A Kudancin Mozambique
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31406-an_hallaka_'yan_tawaye_9_a_kudancin_mozambique
Jami'an 'yan sandar kasar Mozambique sun sanar da hallaka 'yan tawaye 9 a kudancin kasar
(last modified 2018-08-22T11:31:55+00:00 )
Jun 04, 2018 06:27 UTC
  • An Hallaka 'Yan Tawaye 9 A Kudancin Mozambique

Jami'an 'yan sandar kasar Mozambique sun sanar da hallaka 'yan tawaye 9 a kudancin kasar

Cikin wata sanarwa da suka fitar a jiya Lahadi, jami'an 'yan sandar kasar Mozambique sun sanar da hallaka 'yan tawaye 9 a jahar Cabo Delgado dake arewacin kasar cikin wani sumame da suka kai ranar asabar din da ta gabata.

Sanarwar ta ce sun kai sumamen ne bayan wani hari da 'yan tawaye suka kai kauyuka biyu na jahar Cabo Delgado a ranar 27 ga watan Mayun da ya gabata, inda suka kashe mazauna kauyukan kimanin goma.

Jami'an 'yan sandar sun kara da cewa a yayin kai sumamen sun samu makamai masu yawa a maboyar 'yan tawayen.

A cewar hukomomin kasar Mozambique, a watan Oktoban shekarar 2017 din da ta gabata, 'yan tawayen sun mamaye wani gari na cikin jahar ta Cabo Delgado, kuma ya zuwa yanzu an kame sama da mutane 300 da ake zarki da alaka da kungiyar 'yan tawayen.