Firayi Ministan Kasar Madagaska Yayi Murabus Daga Mukaminsa
(last modified Mon, 04 Jun 2018 18:21:33 GMT )
Jun 04, 2018 18:21 UTC
  • Firayi Ministan Kasar Madagaska Yayi Murabus Daga Mukaminsa

Firayi ministan kasar Madagaska, Olivier Mahafaly, ya sanar da yin murabus dinsa don girmama umurnin da kotu ta bayar na kafa gwamnatin hadin kan kasa a kasar da nufin kawo karshen rikicin siyasa da ya kunno kai a kasar.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa, ya ba da labarin cewa firayi minista Olivier Mahafaly ya sanar da murabus din nasa ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a yau din nan inda ya ce ya mika takardar murabus dinsa ga shugaban kasar Hery Rajaonarimampianina don share fagen kafa gwamnatin hadin kan kasa a kasar.

A watan da ya gabata ne dai shugaban Rajaonarimampianina ya amince da sabuwar dokar zaben kasar wacce ta share fagen tsayawar jagoran 'yan adawan kasar  Marc Ravalomanana tsayawa takara sabanin tsohuwar dokar wacce ta hana shi tsayawa lamarin da ya haifar da rikici da zanga-zangogi a kasar.

A kwanakin baya ne dai babban kotun kasar ta bukaci shugaban kasar da ya rusa gwamnatin kasar da kuma kafa wata sabuwar gwamnati wacce za ta sami goyon bayan dukkanin jam'iyyun siyasa na kasar.