Amurka Ta Hallaka Mayakan Al-Shabab 27 A Somaliya
Rundunar sojin Amurka ta ce harin da dakarunta na musammam suka kai ta sama, ya hallaka mayakan al-Shabab 27 a arewacin Somaliya.
Sanarwar da rundunar sojin Amurka dake aiki a Afrika (AFRICOM) ta fitar, ta ce an kai harin na ranar Asabar ne da hadin gwiwar gwamnatin Somaliya, a kudu maso yammacin birnin Bosaso.
Harin dai bai shafi fararen hula ba, a cewar sanarwar ta AFRICOM..
Wannan Harin, dai shi ne na baya-bayan nan cikin jerin hare-haren da dakarun Amurka ke kaiwa kasar dake yankin kahon Afrika da hadin gwiwar dakarun Tarayyar Afrika.
Ana kai galibin ire iren wadanan hare-haren ne kan jagororin kungiyar al-Shabab da sansanoninsu dake kudancin Somaliya, inda har yanzu kungiyar ke rike da wasu yankuna.