Gwamnatin Masar Ta Yi Murabus
Fadar shugaban kasar Masar ta sanar da murabus din Piraministan kasar Sherif Ismail da gwamnatinsa a daren jiya talata.
Kamfanin dillancin labaran Pars ya nakalto Bisam Raadi kakakin fadar shugaban kasar Masar a daren jiya talata na cewa Piraminstan kasar Sherif Ismail ya meka takardar murabus din gwamnatinsa ga shugaba Abdulfatah Al-Sese.
A tsarin kasar Masar idan aka sake zaben sabon shugaban kasa, dole ne tsohuwar gwamnati ta yi murabus, sannan zababben shugaban kasar ya sake tura sunayen sabuwar gwamnatinsa ga Majalisar dokokin kasar.
A karshen watan Maris da ya gabata ce al'ummar kasar Masar suka sake zaben shugaban kasar Abdulfatah Al-sese a karo na biyu, inda ya samu kashi 97 % a kuri'u miliyan 21 da aka kada.