Gwamnatin Masar Ta Mika Takardar Murabus Dinta Ga Shugaba Sisi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31470-gwamnatin_masar_ta_mika_takardar_murabus_dinta_ga_shugaba_sisi
Gwamnatin kasar Masar karkashin jagorancin firayi minista Sherif Ismail ta mika takardar murabus dinta ga shugaban kasar Abdulfattah Al-Sisi a jiya Talata bayan rantsar da shi da aka yi a wa'adi na biyu na shugabancin kasar ta Masar.
(last modified 2018-08-22T07:01:56+00:00 )
Jun 06, 2018 05:53 UTC
  • Gwamnatin Masar Ta Mika Takardar Murabus Dinta Ga Shugaba Sisi

Gwamnatin kasar Masar karkashin jagorancin firayi minista Sherif Ismail ta mika takardar murabus dinta ga shugaban kasar Abdulfattah Al-Sisi a jiya Talata bayan rantsar da shi da aka yi a wa'adi na biyu na shugabancin kasar ta Masar.

A wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar a daren jiya, ta ce firayi minista Sherif Ismail ya mika takardar murabus dinsa da kuma 'yan majalisar ministocinsa ga shugaba Al-Sisi din a matsayin wani mataki na kafa sabuwar gwamnati a kasar, to sai dai firayi ministan zai ci gaba da rike mukamin nasa a matsayin mai rikon kwarya har lokacin da za a kafa sabuwar gwamnati.

A zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Maris din da ya gabata shugaba Sisi ya sami gagarumin rinjaye inda ya sami kashi 97.08 cikin dari na kuri'un da aka kada inda ya sami damar ci gaba da mulkin kasar a wa'adin mulki na biyu.

A bisa al'ada dai a duk lokacin da aka zabi sabon shugaban kasa, gwamnatin kasar ta kan yi murabus don ba da damar kafa  wata sabuwar gwamnatin.