Shugaban Kasar Masar Ya Zabi Ministan Gidaje A Matsayin Sabon Priministan Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31532-shugaban_kasar_masar_ya_zabi_ministan_gidaje_a_matsayin_sabon_priministan_kasar
Shugaban kasar Masar Abdulfatah Assisi ya zabi ministan gidaje a matsayin sabon Priministan kasar bayan da gwamnatin Sherif Isma'ila ta kawo karshen aikinta kamar yadda aka saba, idan za'a fara sabon wa'adi na mulkin shugaban kasa.
(last modified 2018-08-22T07:01:56+00:00 )
Jun 08, 2018 02:12 UTC
  • Shugaban Kasar Masar Ya Zabi Ministan Gidaje A Matsayin Sabon Priministan Kasar

Shugaban kasar Masar Abdulfatah Assisi ya zabi ministan gidaje a matsayin sabon Priministan kasar bayan da gwamnatin Sherif Isma'ila ta kawo karshen aikinta kamar yadda aka saba, idan za'a fara sabon wa'adi na mulkin shugaban kasa.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a lokacin ganawarsa da Dr. Mustafa Madboly a fadar shugaban kasa a jiya Alhamis. Kafin haka dai Dr Mostafa Madbouly ya na rike da kujerar ministan gidaje tun farkon gwamnaton Priminista Sherif Isma'ila, sannan ya tabe rike kujerar Priminister na wucin gadi a lokacinda Isma'ila ya ke jinya tsakanin watan Nuwamban shekara ta 2017 zuwa watan Jenerun wannan shekara.

Kakakin Fadar shugaban kasar Masar Bassam Radi ya fadawa yan jarida ce Dr Mostafa Madbouly dan shekara 52 a duniya ya amince zai kafa sabuwar gwamnati a sabon wa'adin shugaban kasa Abdul fata Assisi na wasu shekaru 4.

A ranar Asabar da ta gabata ce aka rantsar da shugaba Abdulfata Assisi dan shekara 63 a duniya bayan ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar watanni ukku da suka gabata da kashi 97% na yawan kuri'un da aka kada. Shugaban ya lashe  zaben ne ba tare da jam'iyyun adawa na gaskiya ba.