Nijar : Kotun Tsarin Mulki Ta Amunce Da Sake Zaben Mahamadu Issoufou
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3172-nijar_kotun_tsarin_mulki_ta_amunce_da_sake_zaben_mahamadu_issoufou
kotun tsarin mulki a jamhuriya ta amunce da zaben shugaban kasa zagaye na biyu da shugaban kasar Mahamadu Isufu ya lashe da kashi 92.51% .
(last modified 2018-08-22T06:58:03+00:00 )
Mar 30, 2016 13:28 UTC
  • shugaban kasar Nijar Mahamadu Isufu
    shugaban kasar Nijar Mahamadu Isufu

kotun tsarin mulki a jamhuriya ta amunce da zaben shugaban kasa zagaye na biyu da shugaban kasar Mahamadu Isufu ya lashe da kashi 92.51% .

A kudirin da kotun ta fitar yau Laraba wanda shugabar kotun Kadidjatou Abdoulaye Ly ta karanto ta ce tayi na'am da kuma amuncewa da zaben da aka gudanar a ranar 20 ga wata tare da ayyana Mahamadu Issufu a matayin sabon shugaban kasar a wa'adin mulkin sa na biyu da zai fara daga ranar biyu ga watan Afrilun gobe.

kotun ta ce dan takara Hama Amadu ya samu kashi 7,49% yayin da Mahamadu Issufu ya samu kashi 92.51% na kuri'un da aka kada wanda hakan ya bashi damar lashe zaben.

Idan dai ana tune 'yan adawa a wannan kasar sun kauracewa zaben tare da yin watsi da sakamakon sa saboda a cewar su magudin da aka tafka tun a zaben farko wanda kuma kotun tsarin mulkin bata saurari korafe-korafen su ba.