Sabuwar Gwamnatin Kasar Masar Ta Yi Rantsuwar Kama Aiki
Sabuwar gwamnatin kasar Masar karakshin Priminista Mustafa Madluli ta yi rantsuwar kama aiki a gaban shugaban kasa Abdulfatah Assisi.
Tashar talabijin ta Almayadiin ta bayyana cewa Mustafa Madluli tare da majalisar ministocinsa sun yi rantsuwar kama aiki a gaban shugaban.
Labarin ya kara da cewa Janar Mohammad Ahmad Zaki, babban komandan sojojin masu tsaron fadar shugaban kasa shi ne ministan tsaro na 25 tun bayan samun 'yencin kai a shekara 1952 a sabuwawa gwamnatin.
Shafin yanar gizo na "Alyaumussabe" ya kara da cewa Janar Mohammad Ahmad Zaki tare da rundunarsa sun bin umurnin shugaba Mursi na amfani da karfi wajen tarwatsa taron yan adawa a lokacinda suka yi cincirindo a fadar shugaban kafin a yi masa juyin mulki. Banda haka yana daga cikin shaidun da aka gabatar a gaban kotu na tuhumar tsohon shugaban kasar da aikin leken asiri wa kasashen waje