Jami'an Tsaron Nijar Sun Kame Ton Uku Na Tabar Wiwi A Kasar
Rahotanni daga kasar Nijar sun bayyana cewar jami'an tsaron kasar sun sami nasarar kame ton uku na tabar wiwi da aka shigo da ita kasar, a wani abu da ake ganinsa a matsayin mafi girman nasarar da jami'an tsaron suka samu a wannan fagen.
Rahotannin sun jiyo ministan cikin gidan na Nijar, Bazoum Muhammed, yana fadin cewa ana zargin cewa an shigo da tabar wiwi din ne daga kasar Moroko wanda kuma kudinta ya kai dala miliyan 5.
Jami'an tsaron dai suna tsare da mutane 12 da ake zargin suna da hannu cikin wannan badakalar shigowa da tabar wiwi din da suka hada da wasu daga Nijeriya, Mali, Moroko da Aljeriya sannan kuma ana ci gaba da tsare su a gidan yari a birnin Yamai, babban birnin kasar ta Nijar.
Cikin watannin baya-bayan nan dai kasar ta Nijar ta sami nasara a fadar da take yi da fataucin muggan kwayoyi inda ko a watan Mayun da ya gabata, 'yan sandan kasar sun kwace kimanin ton 29 na magunguna na jabu da aka shigo da su kasar.