MDD Ta Yi Gargadi Kan Ambaliyar Ruwa A Kasar Nijer
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31868-mdd_ta_yi_gargadi_kan_ambaliyar_ruwa_a_kasar_nijer
Ofishin Kula da Agaji na MDD dake birnin Yamai na kasar Nijer ya yi gargadi kan aukuwar ambaliyar ruwa a cikin wannan shekara da ka iya jefa rayuwar duban mutanan kasar cikin matsala.
(last modified 2018-08-22T11:32:00+00:00 )
Jun 20, 2018 06:26 UTC
  • MDD Ta Yi Gargadi Kan Ambaliyar Ruwa A Kasar Nijer

Ofishin Kula da Agaji na MDD dake birnin Yamai na kasar Nijer ya yi gargadi kan aukuwar ambaliyar ruwa a cikin wannan shekara da ka iya jefa rayuwar duban mutanan kasar cikin matsala.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto ofishin kula da kai agajin gaggawa na MDD dake birnin Yamai na jamhoriyar Nijer na cewa akwai yiyuwar samun ambaliyar ruwa a kasar daga cikin watan yuni zuwa watan satumba na wannan shekara ta 2018 da muke ciki, musaman ma a yankunan Dosso da birnin Yamai, da hakan na iya jefa rayuwar mutane sama da dubu 170 na kasar cikin matsala.

Sanarwa ta Ofishin kula da agajin gaggawa na MDD dake birnin yamai ta ce akwai yiyiwar za a zabka ruwan sama mai yawa a cikin watanin yuni zuwa Satumba na shekara bana a yankuna daban daban na kasar Nijer, da hakan na iya janyo ambaliyar ruwa a kasar.

A shekarar 2017 da ta gabatar, kimanin mutum 56 ne suka rasa rayukansu a kasar ta Nijer daga cikinsu akwai mutane 20 daga mazauna birnin yamai sanadiyar ambaliyar ruwan sama a kasar sannan ya janyo hasara ga mutane sama da dubu 206 a fadin kasar.