Rikicin Kabilanci Ya Ci Rayukan Mutane 27 A Kasar Habasha
Jun 24, 2018 12:49 UTC
Kamfanin dillancin labarun Xinhua ya ambato shugaban 'yan sanda a yankin Fissheha Garedewe ne ya sanar da cewa an yi fada a tsakanin kabilun Sidama da Wolaita.
Sanarwar ta ce baya ga mutane 27 da aka kashe, an jikkata wasu fiye da 600,000.
Garedewa ya kara da cewa; Tuni an kame mutanen da suke da hannu a cikin rikicin, sannan kuma ya yi ga mutane da su ba su hadin kai a ci gaba da bincken da suke yi.
A farkon watan Yuni ma an yi wata taho mu gamar a tsakanin wadannan kabilun biyu a garin Awasa inda ya ci rayukan mutane 10.
Sidama da Wolaita su na cikin manyan kabilu a kudancin kasar, sai dai alaka a tsakaninsu ba ta da kyau.
Tags