Shugaban Kasar Ghana Ya Haramta Wa Manyan Jami'an Kasar Tafiya Waje
(last modified Tue, 26 Jun 2018 11:12:31 GMT )
Jun 26, 2018 11:12 UTC
  • Shugaban Kasar Ghana Ya Haramta Wa Manyan Jami'an Kasar Tafiya Waje

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya haramta wa dukkanin ministoci, mataimakan ministoci, shugabannin kanana hukomomi da na jihohi bugu da kari kan shugabannin cibiyoyin gwamnati, in ban da ministan harkokin wajen kasar, yin balaguro zuwa kasashen waje.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne cikin wata doka da ofishinsa ya fitar dauke da sanya hannun shugaban ma'aikata na fadar shugaban kasar Akosua Frema Opare inda yace wannan haramcin zai fara aiki ne ba tare da bata lokaci ba. 

Sanarwar ta cire ministan harkokin wajen kasar Shirley Ayorkor-Botchwey daga haramcin watakila saboda yanayin aikinsa.

A shekara ta 2015 ma dai tsohon shugaban kasar Ghanan John Dramani Mahama ya dau makamancin irin wannan matakin inda ta haramta wa jami'an gwamnatin kasar amfani da bangaren masu kudi, wato bangare mai daraja ta farko na jiragen sama a kokarin da gwamnatin take yi na rage irin kudaden da take kashewa.