An Yanke Hukunci Daurin Shekaru 10 Ga Mashawarcin Ministan Kiwon Lafiyar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32091-an_yanke_hukunci_daurin_shekaru_10_ga_mashawarcin_ministan_kiwon_lafiyar_masar
Kotun hukunta manyan laifuka a Masar ta yanke wa mashawarcin ministan kiyon lafiya hukuncin daurin shekaru 10 a gidan Kaso kan laifin karbar na goro
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jun 27, 2018 14:35 UTC
  • An Yanke Hukunci Daurin Shekaru 10 Ga Mashawarcin Ministan Kiwon Lafiyar Masar

Kotun hukunta manyan laifuka a Masar ta yanke wa mashawarcin ministan kiyon lafiya hukuncin daurin shekaru 10 a gidan Kaso kan laifin karbar na goro

Hukumar gidan radio da talabijin ta kasar Iran ta nakalto majiyar shari'ar kasar Masar na cewa a wannan laraba kotun hukunta manyan laifuka ta kasar karkashin jagorancin mai shari'a Hamad Shukri ta yanke hukunci daurin shekaru 10 a gidan kaso ga Ahmad Aziz mai bawa ministan lafiya na kasar shawara tare kuma da tarar Pond dubu 500 saboda ta same shi da laifin karbar cin hanci.

Har ila yau kotun ta wanke wani da ake zarki da hannu da laifin bisa ayar doka mai lamba 107 na kundin huhuncin kasar Masar.

A cikin watanin baya-byan nan an gurfanar da jami'an gwamnati da dama na kasar a gaban Kotu kan laifin cin hanci da rashawa.