Sama Da Misrawa 240 Ne Aka Sanya A Jerin 'Yan Ta'adda
Masar ta fitar da sunayen mutane sama da 240 da take zarkinsu da shiga cikin kungiyoyin 'yan ta'adda
Kamfanin dillancin labaran Anatolio ya habarta cewa kotun birnin Alkahira ta fitar da sunayen 'yan kasar 241, inda ta zarkesu da kasancewa cikin kungiyar 'yan ta'adda ta wulayatu Sina, wani bangare na kungiyar ISIS a yankin tsibirin Sinai na kasar wadanda suka aiwatar da hare-haren ta'addanci da kuma kashe jami'an tsaron kasar a tsahon shekaru biyar.
Kotun ta ce ta dauke wannan mataki ne na sanya wadannan mutane a cikin jerin 'yan ta'adda, bayan binciken da ta gudanar a kansu, inda bincikenn ya tabbatar da cewa wadannan mutane 241 na kokarin wargaza gwamnatin kasar.
A shekarun baya-bayan nan dai, kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin Sinai sun kai hare-hare da dama kan jami'an tsaro na Sojoji da na 'yan sandar kasar Masar, lamarin da ya yi sanadiyar salwanta rayukan da dama daga cikinsu, wasunsu kuma suka jikkata.