Ana Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnati A Arewacin Marocco
Dubun dubatan mazauna garin Daru-Baida'a ne suka gudanar da zanga-zangar neman a sako jagororin 'yan adawa na yankin.
A jiya Lahadi, Dubun dubatan mazauna garin Daru-Baida'a na arewacin kasar Maroco sun gudanar da zanga-zangar na neman a sako mutanan da gwamnati ta tsare saboda nuna rashin jin dadinsu da yanayin da ake tafiyar da milki a kasar.
Wasu kungiyoyin farar hula da jam'iyun adawa ne suka kira wannan zanga-zanga, da ta samu halartar duban mazauna yaniki, inda suka rika rera taken a gaggauta sako da wadanda ake tsare domin neman 'yancin kasar Maroco da ci gaban talakawa.
Bayan kwashe sama da shekara guda a gidan yari, a ci 'yan kwanakin nan ne wata kotu a Maroco ta yanke hukuncin daurin shekaru 20 ga Nasir Zafzafi shugaban kungiyar masu adawa da gwamnati na yankin Rif, sannan kuma aka yankewa sauran abokaninsa na wannan kungiya mai fafutukar nemawa talakawa saukin rayuwa, su 15 daurin shekaru 15 a gidan Kaso.
A watan Mayun shekarar 2017 din da ta gabata ce jami'an tsaron Maroco suka kama Zafzafi tare da wasu Mutane 20 a yayin gudanar da zanga-zangar nneman sauyi a garin AL-HOCEIMA na yankin Rif kan zargin dagula al'amuran tsaron yankin.