Najeriya / Nijar : Buhari Ya Taya Isufu Murna
-
shugaban Najeriya Muhamadu Buhari
Shugaban tarraya Najeriya Muhamadu Buhari ya taya takwaran sa na Nijar Mahamadu Isufu murna dangane da sake zaben sa a wa'adi na biyu na shugaban kasa.
Wata sanarwa da kakakin fadar shugaban kasa Najeriya Femi Adesina ya sanya ma hannu ta ce, shugaba Buhari na taya Mahamadu Isufu dama al'ummar kasar ta Nijar murna dangane da zabubukan kasar da suka gudana cikin lumana, wanda a cewar sanarwar babban ci gaba ne ga kasar. A Hannu daya sanarwar ta ce Buhari ya ji dadin gayatar da aka aike masa na halartar bikin rantsar da takwaran na sa, saidai ba zai samu damar halarar bikin ba wanda ya zo a daidai lokacin da yake halartar taron kolin tsaron nukiliya karo na hudu dake gudana a birnin Washington na Amurka.
Kazalika sanarwae ta ce Buhari yayi ma Isufu fatan alhairi a sabon wa'adin mulkin sa tare da fatan Allah ya kawo zamen lafiya da konciyar hankali a kasashen biyu.
A gobe Lahadi ne ake sa ran rantsar da sabon shugaban kasar ta Nijar Mahamadu Isufu a sabon wa'adin mulkin sa bayan lashe zaben shugaban kasar zagaye na biyu wanda 'yan adawa suka kauracewa da gagarimun rinjayen da ba'a taba yin sa ba a tarihin kasar.