Cacar Baki Tsakanin Sudan Ta Kudu Da Wasu Kasashen Yamma
Cacar baki ta kaure tsakanin Sudan ta Kudu da wasu kasashen yamma hudu, bayan da wasu jami'ansu, suka soki halin da ake ciki a wannan jinjirar kasa dake gabashin AFrika.
Wani babban jami'i a ma'aikatar harkokin cikin gidan Sudan ta Kudu, ya zargi kasashen Amurka da Biritaniya, da Norwey da kuma Faransa, da shishigi a harkokin cikin gidan kasar.
Wannan dai ya biyo bayan da kasashen suka yi allawadai da tsawaita wa'addin mulki ga Shugaban kasar ta Sudan, Salva Kiir, da kuma ci gaba da take hakkin bil adama a kasar.
Jami'in ya ci gaba da cewa kasashen na yamma basu da hakkin sukar majalisar dokokin kasar, balle shawartar shugaban kasar ya yi watsi da kudirin majalisar.
A makon da ya gabata ne, majalisar dokokin Sudan ta Kudun, ta kada kuri'ar yin na'am da kudirin tsawaita wa'adinsu, da kuma na mulkin shugaban kasar da wasu mukaranbansa biyu da kuma na gwamnonin jihohin da shekaru ukku, wanda zai basu damar ci gaba da rike mukamminsu har zuwa shekara 2021.