Za'a Gudanar Da Zaben Shugaban A D.R.Congo Kamar Yadda Aka Tsara
Shugaban kasar D-Congo Joseph Kabila ya bayyana cewa za'a gudanar da zaben shugaban kasa a cikin watan Decemba na wannan shekarar kamar yadda aka tsara amma bai bayyana ko zai sabawa kundin tsarin mulkin kasar ya tsaya takara ba.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto shugaban yana fadara haka a jiya Alhamis a wani jawabinda ya yiwa mutanen kasar ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar ce zata bada kudaden gudanar da zaben don kaucewa korafe korafen kasashen waje kan jinkiran da aka samu na gudanar da shi.
Shugaban oseph Kabila dai ya karbin ikon kasar D- Congo ne tun shekara ta 2001 bayan kisan mahaifinsa, idan ya gudanar da zaben kamar yadda aka tsara to shi ni karon farko kenan da aka gudanar da zabe a kasar D- Kongo tun bayan samun 'yencin kai a shekara 1960.
Manya manyan kasashen duniya da kuma Majalisar dinkin duniya duk suna takurawa shugaban don ya sauka bayan shugabancin na shekarau 21 kan kujerar shugabancin kasar.