Ambaliyar Ruwa Ya Ci Rayukan Mutane 13 A Nijer
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i32407-ambaliyar_ruwa_ya_ci_rayukan_mutane_13_a_nijer
A jamhoriyar Nijer, kimanin mutane 13 ne suka rasu rayukansu a wasu sassan kasar
(last modified 2018-08-22T11:32:08+00:00 )
Jul 20, 2018 18:12 UTC
  • Ambaliyar Ruwa Ya Ci Rayukan Mutane 13 A Nijer

A jamhoriyar Nijer, kimanin mutane 13 ne suka rasu rayukansu a wasu sassan kasar

Ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD, OCHA, a Nijar, ya fitar da rahoton cewa, zuwa ranar 18 ga watan Yulin nan mutane 13 ne suka rasa rayukansu, kana wasu 17,000 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa da aka fuskanta a wasu sassan kasar ta Nijar.

Rahoton ya ce ambaliyar ruwan ta yi awan gaba da ekta 400 na filayen noma, da kuma dabbobi sama da 24,000.

Jihohin da ambaliyar ruwan ta shafa sun hada da Maradi Agadas, da kuma Diffa.

Kafin hakan dai, masana yanayi da Majalisar dinkin Duniya sun hasashen cewa a wannan shekara za a samu ambaliyar a wasu yankunan kasar, musaman ma a jihohin Yamai, Agadez, Tawa da Maradi.