Sojojin Masar Sun Kadamar Da farmaki A Garin Rafah
A wannan Lahadi, dakarun tsaron Masar sun kadamar da gagarimin farmaki a garin Rafah dake jihar Sinai kusa da kan iyakar yankin zirin Gaza na Palastinu.
Kamfanin dillancin labaran Fars ya habarta cewa biyo bayan harin roka da wasu mutane da ba san ko su waye ba suka kaiwa dakarun tsaron Masar a yankin Rafah da ya yi sanadiyar hallakar Soja guda tare da jikkata wasu na daban, a wannan lahadi, dakarun tsaron Masar sun kadamar da wani gagarimin farmaki a garin na Rafah.
Jaridar Al-arabie jadeed a shafinta na yanar gizo ta rubuta cewa, Rundunar tsaron Masar ta tura karin dakarunta da kayan yaki zuwa garin Rafah.
A jiya Asabar ne, Wasu gungun 'yan bindiga sun kai harin wuce gona da iri kan wata motar sojin Masar mai sulke a lardin Tsibirin Sina na Masar kusa da kan iyaka da yankin Zirin Gaza na Palasdinu da makamin roka , inda harin ya yi sanadiyyar mutuwar soja guda tare da jikkata wasu biyu na daban.
Tun daga watan Favrayun shekarar da ta gabata ce, dakarun tsaron Masar suka kadamar da farmaki, ta kasa, sama da ruwa a garinruwan dake jihar Tsibirin Sinai na kasar da nufin kawo karshen kungiyoyin 'yan ta'adda.