Shugaban Kasar China Ya Gargadi Amurka Kan Yakin Kasuwanci Da Ta Fara
(last modified Thu, 26 Jul 2018 12:01:59 GMT )
Jul 26, 2018 12:01 UTC
  • Shugaban Kasar China Ya Gargadi Amurka Kan Yakin Kasuwanci Da Ta Fara

Shugaban Kasar China Xi Jinping ya gargadi Amurka kan yakin kasuwanci da ta fara, ya kuma kara da cewa abin zai cutar da kowa.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar ta China ta nakalto shugaban yana fadar haka a taron kungiyar Bricks da ake gudanarwa a halin yanzu a kasar Afrika ta kudu.

Shugaban ya bayyana haka ne bayan da Amurka ta dorawa kayakin kasywancin kasar China da ake shigo da su Amurka haraji wanda ya kai dalar Amurka bullion 34, sannan tana shirin dorawa kasashen turai ma irin wannan haraji.

Banda haka shugaban ya yi kira ga gwamnatin Amurka ta dawo cikin yerjejeniyar yanayi ta Paris da ta fice a shekarar da ta gabata 

A halin yanzu dai ana ci gaba da taron kasashe 5 na kungiyar Bricks a birnin Jorhanasburg na kasar Afrika ta kudu. Kasashen din hada da China India, Brazil, Afrika da Kudu da kuma Rasha.