An Yi Wa Tsoffin Ministoci Biyu Daurin Talala A Kasar Masar
(last modified Mon, 30 Jul 2018 06:50:25 GMT )
Jul 30, 2018 06:50 UTC
  • An Yi Wa Tsoffin Ministoci Biyu Daurin Talala A Kasar Masar

Kafafen yada labarai na kasar Masar sun bayyana cewa an yi wa tsoffin ministoci biyu daurin talala a wasu gidaje a birnin Alkahira.

Shafin yanar gizo na "Arab 21" ya bayyana cewa ya sami labari daga wasu wadanda suke da masaniya kan lamarin kan cewa shugaban kasar ta Masar Abdul Fattah Assidi ya bada umurnin yi wa tsohon ministan harkokin cikin gida Sidqy Subhy, da kuma tsohon ministan tsaron kasar Mjdy Abdulgaffar tare da iyalansu daurin tatala a wasu wuraren da ba'a sani ba. 

Majiyar ta kara da cewa tun bayan kafa sabuwar gwamnati a cikin watan Yuni shekara ta 2018 ne aka dauke Sidqi Subhi da kuma Majd Abdulgafur da iyalansu zuwa wasu wuraren da ba'a sani ba har yanzun. 

Babu wanda ya san dalilan tsare wadannan tsoffin ministoci da kuma iyalansu. Labarin ya kammala da cewa hatta danginsu basu san ida suke ba.