An Tsawaita Aikin Dakarun Turai A Afirka Ta Tsakiya
(last modified Tue, 31 Jul 2018 07:26:34 GMT )
Jul 31, 2018 07:26 UTC
  • An Tsawaita Aikin Dakarun Turai A Afirka Ta Tsakiya

Kungiyar tarayar Turai ta tsawaita ayyukan dakarunta na tsawon shekaru biyu a kasar Afirka ta Tsakiya

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga birnin Brussel ya habarta cewa a jiya Litinin Majalisar kungiyar tarayyar Turai ta bayyana cewa dakarun tsaron kungiyar EU dake bayar da horo ga dakarun tsaron Afirka ta tsakiya za su ci gaba da kasancewa a kasar har zuwa ranar 19 ga watan Dicembar 2020.

Baya ga wannan, kungiyar EU din ta ce za ta kara yawan dakarunta masu bayar da shawara kan harakokin tsaro a kasar Afirka ta tsakiyan.

Kungiyar EU din ta kara da cewa, bayan Ma'aikatar tsaro da manyan jami'an tsaron kasar, Dakarun nata za su dinga taimakawa gwamnatin Alfirka ta tsakiya da shawarwari kan matakin da ya kamata ta dauka domin kawo karshe rikicin kabilanci da addini a kasar.

Tun a shekarar 2013 ne kasar Afirka ta tsakiyan ta fara  rikicin kabilanci da na addini, lamarin da ya salwanta rayukan duban  al'ummar kasar.