Nijar Na Bikin Cika Shekaru 58 Da Samun 'Yancin Kai
Yau Juma'a 3 ga watan Agusta 2018, Kasar Nijar ta cika shekaru 58 da samun 'yankin kai, daga turawa 'yan mulkin mallaka na Faransa.
Shugaban kasar na farko Djori Hamani ne ya sanar da samun 'yancin a rana irin ta yau 3 ga watan Agusta na 1960.
A jajibirin wannan ranar shugaban kasar mai ci Isufu Mahamadu, ya yi jawabi ga 'yan kasar, inda ya tabo batutuwa da dama, da suka hada da matsalar tsaro, shirye shiryen zabuka masu zuwa, halin da sha'anin ilimi ke ciki.
Kan batun tsaro shugaban kasar ya ce an karya laggon kungiyar Boko Haram, saidai abunda ba'a rasa ba.
Kan sha'anin ilimi kuwa, shugaban kasar ya dora alhakin tabarbarewa ilimim, ga yaje yajen aiki da kaurace wa azuzuwa da aka fuskanta, ba wai rashin kwarewar malumman makarantun ba ne kawai.