An karfafa matakan tsaro a arewa maso gabashin Najeria
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3265-an_karfafa_matakan_tsaro_a_arewa_maso_gabashin_najeria
Dakarun tsaron Najeria sun karfafa matakan tsaro a shiyar arewa maso gabashin kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:04+00:00 )
Apr 01, 2016 13:36 UTC
  • An karfafa matakan tsaro a arewa maso gabashin Najeria

Dakarun tsaron Najeria sun karfafa matakan tsaro a shiyar arewa maso gabashin kasar

Kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar China ya nakalto Abdull..Ghana shugaban kungiyar dakarun sa kai na Najeria na cewa su kara yawan dakaru dubu biyar a jahohin Adamawa, Borno , Yobe dake fama da rikicin boko haram a Arewa maso gabashin kasar, kuma hakan na a matsayin cike gurbin Dakarun tsaron da suka rasa rayukansu a filin daga.

Abdul..Ghana ya ce cikin shekarar 2015 da ta gabata , dakarun tsaron kasar sun kwato gariruwa da kuma kauyuka da dama da kungiyar boko haram din ta mamaye a shiyar arewa maso gabashin kasar.

Har ila yau a cikin 'yan watanin nan Gwamnatin ta Najeria ta rarraba jami'an 'yan sanda sama da dubu shiga a Jihohin Adamawa, Borno da Yobe dake shiyar Arewa maso gabashin kasar.cikin shekaru 6 da suka gabata, rikicin Boko haram ya yi sanadiyar duban Mutane a Najeria, baya ga kasar, rikicin boko haram din ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a kasashen Nijer, Kamaru da Tchadi dake makobtaka da Najerian, inda ko a safiyar jiya Alkhamis ma, mayakan na boko haram suka kashe Sojojin Nijer 6 tare da jikkata wasu uku na daban.