An Kori Ministan Makamashi A Ghana
(last modified Tue, 07 Aug 2018 10:31:37 GMT )
Aug 07, 2018 10:31 UTC
  • An Kori Ministan Makamashi A Ghana

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya sallami ministan makamashin kasar Boakye Agyarko daga mukaminsa ba tare da bata lokaci ba.

Wata sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar, ta ce, an umurci koraren ministan da ya damka ragamar ofishinsa ga John Peter Amewu, ministan filaye da albarkatun kasa, wanda zai kasance ministan makamashin kasar na wucin gadi.

Kawo yanzu ba'a bayyana dalilin sallamar mista Agyarko ba, amma wasu rahotanni daga kasar sun ce sallamar jami'in yana da nasaba da yunkurin da ma'aikatar makamashin kasar ta yi mai cike da sarkakiya na sauya alkaluman yarjejeniyar kwangilar aikin samar da makamashi wanda aka kulla tsakanin tsohuwar gwamnatin kasar Ghanar da wani kamfanin hadaddiyar daular larabawa UAE mai sansanoni a Afrika da yankin gabas ta tsakiya (AMERI) a shekarar 2015, wanda ya kai dalar Amurka miliyan 510.