Masu Bada Agaji A Kasar Afrika Ta Tsakiya Na Fuskantar Barazanar Kisa
Masu bada agaji a kasar Afrika ta tsakiya suna fuskantar barazanar kisa a lokacinda yawan yan agajin da aka kashe yake karuwa.
Kamfanin dillancin labaran Xinhuwa na kasar China ya nakalto Najat Rushdi mataimakin shugaan rundunar sojojin tabbatar da zaman lafiya ta Majalisar dinkin duniya a kasar Afrika ta tsakiya wacce ake kira MINUSCA ya na bayyana haka. Ya kuma kara da cewa masu bada agaji 6 ne aka kashe daga farkon wannan shekara ya zuwa yanzu a kasar Afrika ta tsakiya.
Rushdi ya kara da cewa matsalolin tsaro suna nan a duk fadin kasar Afrika ta tsakiya wanda ya zuwa yanzu ya tilastawa kungiyoyin bada agaji 15 suka dakatar da ayyukan bada agaji a yankuna 12 na kasar daga watan Afrilun da ya gabata.
Rahoton ya kara da cewa yawan sace-sace da kwasar ganimar kayakin kungiyoyin bada agaji a kasar ya kara yawa a cikin yan watannin da suka gabata. Kuma mayakan kungiyoyi dauke da makamai daban daban a kasar ne suke yin hakan.