Zimbabwe Na Daukar Matakai Na Fuskantar Takunkumin Amurka
(last modified Thu, 23 Aug 2018 06:40:15 GMT )
Aug 23, 2018 06:40 UTC
  • Zimbabwe Na Daukar Matakai Na Fuskantar Takunkumin Amurka

Gwamnatin kasar Zimbabwe tana daukar matakai na fuskantar takunkumin Amurka, ta hanayar yin amfani da arzikin da Allah ya hore mata, da kuma kara fadada mu'amalarta da wasu kasashen.

A wata zantawa da ya yi da kamfanin dillancin labaran reauters a jiya, Dr Prosper Chitambara masani kan harkokin tattalin arzikin kasashen Afrika ya bayyana cewa, sakamakon irin matakan da Amurka take ci gaba da dauka ta fuskar tattalin arziki a kan kasar Zimbabwe, wannan ya sanya gwamnatin kasar ta kara kaimi wajen dogaro da arzikinta na cikin gida, musamman ma harkokin noma.

Ya ce baya ga haka kuma,a  halin yanzu Zimbabwe ta kara samun wasu sabbin abokai da take yin mu'amala da su a gabashin duniya, wadanda suke kulla yarjejeniyo da kasar domin amfanin junasu.

A cikin watan mayun da ya gabata ne dai shugaban Amurka Donald Trump ya sa hannu kan kara sabunta takunkumin tattalin arziki a kan kasar Zimbabwe, bisa hujjar cewa har yanzu dimukradiyya ba ta nuna a kasar ba.

Shugaba Emmerson Mnangagwa na Zimbabwe ya yi al'ummar kasar alkawalin cewa, nan ba da jimawa kasar za ta samu gagarumin canji ta fusktar kautatar tattalin arzikinta.