An Hallaka Sojojin Hayar Saudiya Sama Da 40 A Yammacin Kasar Yemen
Ma'ikatatar tsaron kasar Yemen ta sanar da hallaka tare da jikkata sojojin hayar Saudiya sama da 100 a yammacin kasar
Cikin wani rahoto da ta fitar a wannan alhamis, tashar talabijin Almasira ta nakalto ma'aikatar tsaron Yemen na cewa Sojojin sun fada cikin tarkon Sojoji da dakarun sa kai na kasar Yemen a kusa da kasuwar Aljabliya dake yankin Attahita na tsibirin yammacin kasar, inda aka hallaka 46 tare da jikkata 57 daga cikinsu.
Ma'aikatar tsaron Yemen din ta ce ko baya da hakan Dakarun kasar sun tarwatse wasu motocin yaki 9 na sojojin hayar Saudiyar a kusa da kasuwar Aljabliya.
A ci gaba da mayar da martani kan harin wuce da kawancen Saudiyar ke kaiwa kan Al'ummar kasar yemen, sojoji da dakarun sa kai na yemen sun hallaka sojojin hayar saudiya a arewacin yankin kan iyala na Maidy dake jahar Aljauf.
A bangare guda kuma wani Bam ya tashi da motar sojojin hayar saudiya a yankin Yatmah na jahar Aljauf, lamarin da ya yi sanadiyar hallakar Sojojin hayar saudiyar guda 4.