An Kashe Yan Ta'adda 4 A Yankin Sinaa Na Kasar Masar
(last modified Sat, 25 Aug 2018 18:58:20 GMT )
Aug 25, 2018 18:58 UTC
  • An Kashe Yan Ta'adda 4 A Yankin Sinaa Na Kasar Masar

Wata majiyar Jami'an tsaron kasar Masar ta bada sanarwan kashe yan ta'adda 4 a yankin Sinaa na araewacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Skynews ya nakalto jami'an tsaron kasar masar suna fadar haka a yau Asabar. Sun kuma kara da cewa an kashe mahara guda huda sannan wasu sun guda, a halin yanzu jami'an tsaron suna bin sawunsu.

Labarin ya kara da cewa an kashe jami'an tsaro hudu an kuma raunata wasu a fafatawa da yan ta'addan a mashigarin garin Arish na yankin Sinaa ta Arewa. 

A ciki watannin da suka gabata kungiyoyin yan ta'adda musamma, musamman wacce ake kira walayatu Sinaa ta sha kai hare hare wa jami'an tsaro a yankin wanda ya sa gwamnatin kasar ta gabatar da shiri na musamman don share su daga yankin.