An Zargi Shugaban Amurka Da Kokarin Rusa Tattalin Arzikin Afirka Ta Kudu
(last modified Sun, 26 Aug 2018 07:17:05 GMT )
Aug 26, 2018 07:17 UTC
  • An Zargi Shugaban Amurka Da Kokarin Rusa Tattalin Arzikin Afirka Ta Kudu

Wani masanin tattalin arziki na kasar Afirka ta kudu Ruth Hall ya ce; Zargin da Trump ya yi wa Afirka da kwace filayen fararen fata, manufarsa rusa tattalin arzikin kasar

Ruth wanda malamin jami'ar Westen Cape ne da ke Afirka ta kudu ya fadawa kamfanin dillancin labaran Sputnik cewa; Zargin na Trump ba shi da wani tushe.

Masanin tattalin arzikin na Afirka ta kudu ya kara dacewa; Yin gyara a cikin kasar noma wajibi ne a kasar ta Afirka ta kudu domin kawo karshe tsohon salon mulkin nuna wariya. Ruth ya kuma ce; A zamanin mulkin wariya an raba bakaken fata da su ne masu rinjaye a kasar, da hakkin mallakar filaye da gonaki.

Masanin tattalin arzikin ya kuma bayyana cewa; Da akwai dokoki bayyanannu da ake amfani da su domin kawo sauye-sauye a cikin hakkin mallakar filaye da gonaki.

Tuni da shugaban kasar Afirka ta kudu cyril Ramaphosa ya bada umarnin a kira yi jakadan Amurka a kasar Jessie Lepen domin ya bada jawabi akan maganganun na Trump