An Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zanga A Nijer
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i33116-an_gudanar_da_gagarumar_zanga_zanga_a_nijer
Gamayayyar kungiyoyin fararan hullan da 'yan siyasa na jamhoriyar Nijer sun gudanar da zanga-zangar gami da taron gangami a birnin Yamai.
(last modified 2018-09-09T19:04:32+00:00 )
Sep 09, 2018 19:04 UTC
  • An Gudanar Da Gagarumar Zanga-Zanga A Nijer

Gamayayyar kungiyoyin fararan hullan da 'yan siyasa na jamhoriyar Nijer sun gudanar da zanga-zangar gami da taron gangami a birnin Yamai.

A wannan lahadin ne duban al'ummar jamhoriyar Nijer suka amsa kiran kungiyoyin fararan hullan, wadda kuma wannan ita ce zanga-zanga ta farko da suka shirya tun bayan da aka sallamo su daga gidajen kaso daban-daban bayan wani kamu da aka yi musu na tsawon watanni sakamakon yin wata zanga-zangar da hukumomi suka haramta.

Rahotanni na cewa a wurin wannan baban taron gangami na birnin Yamai, baya ma ga jagororin kungiyoyin fararan hullan, an samu halartar shugaban jam'iyyar MPN Kishin Kasa Ibrahim Yacouba, wanda a watannin baya jam'iyyarsa ta  fice daga gamayyar jam'iyyun da ke mulki a kasar ta Nijar.

Masu zanga-zanga sun soki lamirin mahakumatan kasar ta Nijar, musamman ma kan yadda suka yarda aka girka sansanonin sojojin kasashen waje a kasar, da kuma yadda hukumomin ke tafiyar da lamuransu na mulki.

A jihar Diffa ma da ta yi fama da rikicin Boko Haram an gudanar da zanga-zangar, inda cikin kulawa ta jami'an tsaro masu zanga-zangar suka isa har wajen hukumomi inda suka mika kokensu.