An hallaka wani komandan 'yan ta'adda a kasar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3313-an_hallaka_wani_komandan_'yan_ta'adda_a_kasar_masar
Majiyar tsaron kasar Masar ta sanar da hallaka wani komandan 'yan ta'adda na kungiyar Ajnadu Masar
(last modified 2018-08-22T06:58:04+00:00 )
Apr 02, 2016 23:02 UTC
  • An hallaka wani komandan 'yan ta'adda a kasar Masar

Majiyar tsaron kasar Masar ta sanar da hallaka wani komandan 'yan ta'adda na kungiyar Ajnadu Masar

A cikin wata sanarwa da Majiyar ta fitar jiya Assabar, komandan 'yan ta'addar mai suna Hamam Muhamad na Ajnadu Masar ya hallaka ne a yayin wani sumame a Dakarun tsaron kasar suka kai maboyarsa, bayan da sojojin biyu sun jikkata.

'yan kashe shekaru biyu ana neman Hamam Muhamad,inda sai a jiya Assabar aka samu nasarar hallaka shi a maboyarsa.

Ajnadu Masar wata karamar kungiyar 'yan ta'adda ce da ta dauki yaunin hare-haren baya-bayan nan da aka kai a cikin kasar ta Masar

A bangare guda ,Dakarun tsaron na Masar na ci gaba da kai sumame a yankunan Rafah, sheihu Zuwaid da Al-Arish dake Tsibirin Sina ta Arewa domin karya lagon kungiyoyin 'yan ta'adda.

Tun bayan da aka kifar da Gwamnatin Muhamad Mursi a kasar ta Masar shekarar 2013 , aka samu billar kungiyoyin 'yan ta'adda, inda suka fara kai hare-haren su kan jami'an 'yan sanda da Sojojin a tsibirin Sina ta Arewa.