An Gudanar Da Jana'izar Kofi Anan A Ghana
A wannan Alhamis ne aka binne gawar Kofi Annan a kasarsa ta asali wato Ghana bayan bikin ban-kwana da shugabanni suka yi masa
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa a wannan alhamis ne al'ummar kasar Ghana da sauran shugabani na duniya suka yi jimami na binne gawar tsohon sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan a kasarsa ta haihuwa wato Ghana, bayan bikin ban-kwana da shugabanni daban-daban suka yi masa.
Bikin binne Mr. Kofi Annan wanda aka yi da misalin karfe 8.30 na wannan safiya agogon Ghana, shi ne ya kawo karshen girmamawar da kasar ta shirya masa.
Marigayin ya jagoranci Majalisar Dinkin Duniyar ne tsakanin shekarar 1997 zuwa 2006, mukamin da ya kasance bakar fata na farko da ya rike ta. Kofi Annan ya bar duniya ne a ranar 18 ga watan jiya na Agusta yana da shekaru 80, bayan gajeriyar jinya da ya yi a kasar Switzerland.