Shugaban Kasar Ruwanda Ya Yi Afuwa Ga Fursunonin Siyasa Sama Da 2000.
Kimanin fursiononin siyasa 2000 ne shugaban kasar Ruwanda Paule Kagame ya yi wa afwa.
Tashar radio ta Swahili a nan JMI ta nakalto labarin cewa shugaban Paul Kagame na kasar Ruwanda ya yi Afwa wa fursiononin siyasa kimani dubu 2 daga cikinsu akwai shugaban jam'iyyar adawa ta FDU inkingi, wato Victoire Ingabire.
An kama shugaban jam'iyyar adawa ta FDU ne tun shekara 2010 bayan da ya share shekaru 16 yana gudun hijira a kasar Holand, an kama shi ne a dai dai lokacinda ya dawo kasar da nufin shiga takarar shugabancin kasar ta Ruwanda. Bayan an gurfanar da shi a gaban kotu aka yanke masa hukuncin zaman kaso na tsawon shekaru 15 bayan zarginsa da laifin cin amanar kasa.
Bayan sallamarsa daga gidan yari, Victoire Ingabire ya yaba da afwan da shugaba Kagame yayi masa, ya kuma kara da cewa da alamun harkokin saiyasa a kasar yana kara kyautata.